An dakatar da binciken tarkacen jirgi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dangin fasinjojin jirgin Malaysia sun yi zanga zanga

Hukumar tsaron sufurin ruwa ta Australia ta ce an dakatar da aikin binciken jirgin sama na Malaysia da ya bace saboda rashin kyawun yanayi.

Hukumar ta ce torokon teku ya tilasta wa wani jirgin ruwan sojin Australia janyewa daga yankin da aka gano wasu abubuwa da ka iya zama baraguzan jirgin ne a ranar Litinin.

Tun da fari dai mataimakin ministan harkokin kasashen waje na China, Xie Hangsheng ya bukaci gamsasshiyar hujja daga gwamnatin Malaysia dangane da ikirarin da ta yi cewa jirgin saman ya fadi ne a kudancin tekun India.

Dangin fasinjojin kuma na ci gaba da zanga-zanga a ofishin jakadancin Malaysia da ke Beijing tare da zargin hukumomin Malaysia da sakaci kamar yadda kakakinsu ya shaidawa manema labarai.