Boko Haram: Bam ya fashe a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Boko Haram sun hallaka mutane dama a Borno

An samu fashewar abubuwa biyu a birnin Maiduguri dake jihar Borno a Nigeria, lamarin da ya janyo mutuwar mutane ciki hadda 'yan sanda.

Rahotanni daga babban asibitin birnin sun nuna cewar an kai gawarwakin mutane biyar.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce mutane kusan 11 ne suka rasu ciki hadda 'yan sanda biyar.

Bayanai sun nuna cewar wata mota makare da bam ne ta fashe da safiyar ranar Talata sannan daga bisani wani bam din ya fashe a kusada wajen binciken ababen hawa da 'yan sanda ke yi.

Kungiyar Boko Haram wacce ke da sansaninta a jihar Borno ta janyo hasarar rayuka da dama tare da jikkata mutane da kuma salwantar dukiyoyi.

Karin bayani