kofin duniya tana kasa tana dabo

Ana aiki a filin wasa na Beira
Image caption Magajin garin ya ce ba su da wani zabi na neman kudaden karasa filin wasan

Magajin garin birnin Porte Alegre dake kudancin Brazil, ya ce birnin ba zai samu daukar bakuncin gasar cin kofin duniya ba, idan ba a amince da wata muhimmiyar doka ba.

Jose Fortunati ya ce dole a kada kuri'a a ranar Talata, a kan kudurin doka ta rangwanta haraji ga kamfanonin da za su yi guraren wucin-gadi a gasar.

Ana gaf da kammala filin wasa na Beira dake birnin, amma ana bukatar gina guraren wucin-gadi ga kafafen yada labarai da wadanda suka dauki nauyi da kuma wasu abubuwa da hukumar kwallo ta duniya ke bukata.

Sai dai, ba a kai ga kammala filin wasan daga waje ba, filin da za a yi wasanni biyar, ciki har da wasanni da Faransa, da na Holland da Argentina.