Gobara ta tashi a ofishin CBN a Lagos

Hedkwatar babban bankin Najeriya Hakkin mallakar hoto cbn facebook page
Image caption Hedkwatar babban bankin Najeriya

Gobara ta tashi a reshen ofishin babban bankin Nigeria- CBN dake Lagos, inda wuta ta lalata wani bangare na ginin.

Wakilin BBC da ya ziyarci wajen, ya bayyana cewar wutar ta ci bene hawa na farko da na biyu.

Sai dai ya bayyana cewar 'yan kwana-kwana sun ci karfin wutar.

Kawo yanzu ba a san musababbin tashin gobarar ba, wacce ta shafe fiye da sa'a tana ci kafin a kashe ta.

Hukumomin babban bankin ko kuma jami'an tsaro ba su yi karin haske ba game da lamarin.

A Nigeria ana yawan samun tashin gobara a 'yan shekarunnan musamman a kasuwanni.

Karin bayani