G7: Takunkumin makamashi a kan Rasha

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rasha ma ta maida martani da sanya wa wasu jami'an Amurka takunkumi

Shugabannin kasashe bakwai masu karfin masana'antu na duniya, G7 sun shiga rana ta biyu ta tattaunawa, inda suka fi mai da hankali kan hadewar Rasha da Crimea.

Shugabannin sun kuma yi gargadin cewa za su kara kakaba wa Rasha takunkumi, musamman ta fuskar makamashi, idan ta mamaye wani karin yanki a gabashi ko kudancin Ukraine.

Mataimakin mai bai wa shugaban kasar Amurka shawara kan harkokin tsaro, Ben Rhodes ya ce idan Rasha ba ta sassauta lamarin da ke faruwa a Crimea ba, babu bukatar ci gaba da alaka da ita.

A karon farko tun shekarar 1998, an haramta wa Rasha wakilci a taron, bayan wani taron gaggawa da kungiyar ta fara yi ya amince da yin watsi da tsarin G8 da ya kunshi Rashar.