A duba batun tsaro, in ji Gwamnonin arewa

Shugaban kungiyar gwamnonin arewa Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Babangida Aliyu, Shugaban kungiyar gwamnonin arewa

A Najeriya, gwamnonin jihohin arewacin kasar sun yi wani zama da mahalarta babban taron kasar daga yankin don daidaita irin bukatun da suke so a gabatar a wajen taron kasa.

Gwamnonin dai sun nemi babban taron ya sake nazarin yadda ake rabon arzikin kasar da kuma matsalar tabarbarewar tsaro a arewacin Najeriya da nufin magance matsalar.