Obama da Turai za su gana kan rikicin Ukraine

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Obama na Amurka zai tashi zuwa Netherlands

A yau ne Shugaba Obama za zai gana da shugabannin Tarayyar Turai da dakarun NATO a Brussels domin tattauna rikicin Ukraine.

A jawabin da zai gabatar nan gaba a yau ana sa ran Mr Oama zai jaddada muhimmancin tsaron Tarayyar Turai ga kasar Amurka, sannan zai ja wa Rasha kunne a kan daukar wani mataki nan gaba da ka iya karya dokar kasa da kasa.

Da yake jawabi a jiya talata a birnin Hague Mr Obama ya shaidawa Moscow cewa idan Rasha ta sake yin kutse a cikin hurumin Ukraine, to Amurka da kawayenta na tarayyar turai a shirye suke su aiwatar da matakai wadanda za su raunana tattalin arzikin Rasha ko da abin zai yi illa gare su.

Tun da farko shugaban hukumar tarayyar turai Hoze Manuel Barroso ya ce kasashe 8 masu karfin tattalin arziki za su shirya taron da ake sa ran Rasha ce za ta jagoranta amma babu ita a cikinsa.

Yace ina ganin taron G7 yana da matukar muhimmanci, saboda ya nuna yadda bakin duka yadda kasashen tarayyar turai ya zo daya kan matakin da Rasha ta dauka kan Ukraine da Crimea don haka za mu yi taron ba tare da Rashar ba.

Karin bayani