'Duniya ta juya wa 'yan tawayen Syria baya'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yarima Salman mai jiran gado

Yarima mai jiran gado a Saudi Arabia ya zargi kasashen duniya da juya wa 'yan tawayen Syria baya, a kokarinsu na kifar da gwamnati.

Yarima Salman ya kuma bukaci kasashen duniya su bada gudunmuwar da ta dace don kawar da gwamnatin Shugaba Bashar Al-Assad.

A jawabinsa wajen bude taron koli na kasashen Larabawa, Yarima Salman ya yi kira a sauya yadda ake tunkarar yakin na Syria.

Shi kuwa shugaban 'yan adawar Syria, Ahmed al-Jarba ya bukaci shugabannin Larabawa ne, su mika wa 'yan tawaye kujerar Syria a taron da kuma ofisoshin jakadancin kasar a kasashensu.

Karin bayani