An sami surukin bin Laden da laifin ta'addanci

Sulaiman Abu Ghaith Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An ce Ghaith shi ne kakakin kungiyar al Qaida

Wata kotu a Amurka ta sami wani surukin Osama bin Laden, Sulaiman Abu Ghaith da laifin hada kai domin kashe Amurkawa bayan harin sha daya ga watan Satumba.

Sulaiman Abu Ghaith wanda ke auren babbar 'yar Osama bin Laden, Fatima, an ce shi ne kakakin al-Qa'ida kuma ya nadi sakonnin farfaganda na bidiyo da suke amfani da su wajen jan hankalin sabbin magoya baya.

Shi ne daya daga cikin mafi girman mukami daga cikin wadanda aka danganta da alQa'ida da ya fuskanci shari'a a wata kotu ta farar hula game da tuhumar da ta shafi ta'addanci.

An kama Abu Ghaith wanda dan Kuwaiti ne a kasar Jordan a bara, aka kuma tasa keyarsa zuwa Amurka.

Zai fuskanci yiwuwar hukuncin daurin rai da rai.

Karin bayani