Facebook ya sayi Oculus Rift

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu wasannin bidiyo sun ce Oculus nada farinjini

Facebook ya sanar da sayen Oculus VR , wani kamfanin California wanda ya kware wajen abubuwan wasan bidiyo a kan kusan dala biliyan biyu.

Oculus Rift yana da kamani da "immersive" wanda kamfanin Google ke kerawa, wanda ake wasan bidiyo da sauraron sauti da kuma kallo duk a waje guda da ake makalawa a kunne.

Shugaban Facebook, Mark Zuckerberg, ya ce fasahar Oculus za ta iya "canza yadda muke aiki da sadawar da kuma wasanni".

A halin yanzu tuni mutane suka bada odar sayen Oculus Rift guda dubu 75.

A yarjejeniyar cinikin tsakanin Facebook da Oculus dai, an bada kudi dala miliyan 400 da kuma hannun jarin Facebook na kusan dala biliyan daya da rabi.

Wannan shi ne ciniki na baya-bayannan da Facebook ya kulla, bayan da ya sayi WhatsApp a kan dala biliyan 19.

Karin bayani