Hukumar Hizbah ta tsare mabarata a Kano

Image caption Akwai dubban mabarata a jihar Kano

Hukumar Hizbah ta Jihar Kano a Nigeria ta ce ta tsare daruruwan mabarata a kokarinta na kawo karshen barace-barace a kan titunan jihar.

Hukumar ta Hizbah ta ce wadanda ta tsare hadda kananan yara da kuma nakasassu.

A shekarar da ta gabata ne, majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar haramta bara a kan titi a cikin jihar.

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta ware wasu kudade don tallafawa mabaratan da ta tantancesu, a wani mataki na inganta rayuwarsu.

Sai dai kuma kungiyar nakasassu a jihar ta Kano na adawa da matakin, inda ta ce gwamnati ba ta yi shirin da ya dace ba, kafin ta soma tsare mabaratan.

A halin yanzu dai ba a cika ganin mabarata a kan tituna a jihar Kano ba tun da dokar ta soma aiki.

Karin bayani