Hukumar Hizba ta kama daruruwan Mabarata.

Mabaraci
Image caption Mabaraci

A jihar Kano dake arewacin Najeriya, hukumar Hizba ta ce zuwa yanzu ta kama daruruwan mabarata a jihar, da suka hada da nakasassu da kuma yara almajirai.

Matakin dai wani bangare ne na yunkurin gwamnatin Kano na hana barace-barace a fadin jihar.

A bara ne dai majalisar dokokin jihar ta amince da wani kudirin doka da zai hana yin bara, wanda ya zama doka, inda gwamnatin jihar ke cewa tana ba da tallafin kudi ga wasu mabarata don hana su barar.

To sai dai kungiyar nakasassu ta jihar ta ce gwamnatin ba ta daukar matakan da suka kamata da za su hana barar kamar yadda ya kamata.

Karin bayani