An hango abu kamar tarkacen jirgin Malaysia

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan uwan wadanda suke cikin jirgin suna cikin makoki

Malaysia ta ce sabbin hotunan tauraron dan Adam sun nuna wasu abubuwa fiye da 120 da aka hango a cikin tekun kudancin India wadanda ka iya kasancewa daga jirgin nan ne da ya bace.

Hotunan wadanda Faransa ta samar sun nuna wasu abubuwan da tsawonsu ya kai fiye da mita ashirin.

Wani kwararren jami'in aikin ceto a cikin ruwa John Noble, ya ce idan har za'a iya gano wani abu dake yawo daga cikin tarkacen jirgin to kuwa za'a iya gano rikordar adana bayanan jirgin wato black box.

Sai dai kuma ya ce tekun yana da zurfi sosai kuma kokarin dauko kuttun bayanan zai kasance da matukar wahala musamman idan rikodar black box din ta daina aikewa da sako.

Ya kara da cewar " Za'a iya kwantantawa da tsauni a karkashin teku a saboda haka sai an yi kokarin gano dukkan wani abu mai nasaba da jirgin komai kankantarsa".

Karin bayani