Rabuwar kawuna a babban taron Nigeria

Mahalarta taron kasa a Nijeriya
Image caption Mahalarta taron kasa a Nijeriya

An samu rarrabuwar kawuna tsakanin wakilai masu halartar taron kasa, inda wasu daga arewacin kasar suka fara barazanar kaurace wa taron.

Yadda za'a kada kuri'ar amince wa da duk wani kuduri da aka gabatar a taron, ya janyo zazzafar muhawarar da ta tilasta wa shugaban taron, mai shari'a Idris Kutigi kafa wani kwamiti mai wakilai 50 wadanda za su duba yadda za'a warware takaddamar.

Tsohon Minista wutar lantarki na Najeriya, Injiniya Bello Sulaiman wakili ne daga jihar Sokoto a taron ya ce son zuciya da aka nuna ne tun daga zaben wakilan taron ne ya janyo hakan.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da shugabannin addinin musulunci kasar, suka koka dangane da fifikon da suka ce an nuna wajen zabar mahalarta babban taron kasar.

Karin bayani