Musulmin Nigeria sun koka kan taron kasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarki Muhammad Sa'ad Abubakar

Majalisar koli da ke kula da al'amuran addinin musulunci a Nigeria ta koka wa shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan dangane da fifikon da ta ce an bai wa mabiya addinin Kirista wajen zabar mahalarta babban taron kasar da ake yi.

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar ne ya jagoranci shugabannin kungiyar zuwa fadar shugaban Najeriya don gabatar da wannan koken.

Mabiya addinin kirista 303 ke halartar taron, sabanin takwarorinsu musulmi da aka ba su kujera 183.

Shugaban Najeriya dai ya tabbatar wa mambobin majalisar koli ta addinin musuluncin cewa zai duba kukan nasu da idon basira, kuma zai kasance mai kamanta adalci a kodayaushe.

A watannin baya, kungiyar al'ummar Musulmi a yankin Kudu maso yammacin kasar - MURIC ta yi korafin cewar babu musulmi a cikin tawagar da za ta wakilci shiyyar.

Karin bayani