Obama ya yi karin gargadi ga Rasha

Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto y
Image caption Shugaba Obama ya ce kan kasashen NATO a hade yake

Shugaba Obama ya yi wani jawabi na jaddada 'yancin jama'ar Ukraine na zabar wa kansu makoma.

Ya yi tsokacin ne a ci gaba da kashedi ga Rasha game da shigar da yankin Crimea a cikin kasarta.

Da yake jawabin a Brussels shugaba Obama ya tunatar da Rasha cewa kasashen dake cikin kungiyar kawancen tsaro ta NATO kansu a hade yake.

Ya kara da cewa halin da ake ciki a Crimea ba ya nufin cewa ba za'a sake shiga wani babi na yakin cacar baka ba, amma idan Rasha ta ci gaba da matakin da take kai a yanzu, za ta ci gaba da zama saniyar ware, sannan a kara fadada takunkumin da aka sanya ma ta.

Karin bayani