Tattaunawar keke da keke da 'yan Taliban

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kakakin Taliban, Shahidullah Shahid

An soma tattaunawa gaba da gaba tsakanin gwamnatin Pakistan da 'yan kungiyar Taliban a yankin arewacin kasar dake kan iyaka da Afghanistan.

Tawagar gwamnatin Pakistan ta tafi yankin arewacin Waziristan don ganawa da mayaka na kungiyar Tehreek-i-Taliban ta Pakistan.

Tattaunawar na cikin kokarin Firaiministan Pakistan, Nawaz Sharif na kokarin kawo karshen tashin hankali a kasar lamarin da ya janyo mutuwar dubban mutane.

Gwamnatin kasar ta ce daya daga cikin abubuwan da za ta maida hankali wajen taron shi ne kara wa'adin tsagaita wuta.

Karin bayani