Al-sisi ya yi murabus a Masar

Field Marchal Abdul Fatta al-Sisi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Al-sisi dai ya yi murabus daga mukaminsa saboda samun damatar takarar shugaban kasar Masar da za a fara a wata mai zuwa.

Shugaban hafsan soji kuma ministan tsaron Masar Field Marshal Abdul Fatta al-Sisi ya yi murabus, domin tsaya wa takarar shugabancin kasar da za a fara a wata mai zuwa.

Alsisi ya ce ba za ta sabu ba ace miliyoyin matasan kasar na fuskantar rashin ayyukan yi, kuma kasar na fuskantar barazanar 'yan ta'adda wadanda ke son ganin bayanta.

Abdul Fatta Al-sisi ya kuma gargadi kasashen ketare kan yin katsalandan a harkokin cikin gida na kasar.

Sai dai masu suka na bayyana Al-Sisi, a matsayin wani jami'in soji da ya aiwatar da cin zarafin fararen hula da suka saba wa ra'ayinsa.

Karin bayani