Malaysia: Tauraro ya hango tarkace 300

Ana neman jirgin Malayisa da ya bace
Image caption Jami'an Australia sun ce jiragen ruwa na cigaba da binciken duk da rashin kyawun yanayi

Tauraron dan Adam na kasar Thailand, ya hango abubuwan da ake zaton tarkacen jirgin Malayisa ne da ya bace.

Thailand ta hangi tarkacen da suka kai 300 a kudancin tekun India ne, a ranar 24 ga watan Maris, kwana daya bayan tauraron Faransa ya hango wasu 122.

Sai dai an dakatar da binciken jirgin, a ranar Alhamis saboda rashin kyawun yanayi.

A ranar 8 ga watan Maris ne jirgin mai lamba MH370 ya bace tare da mutane 239 a ciki, kuma kawo yanzu ba a kai ga dauko komai ba daga tarkacen jirgin.