' Zaben rabagardama a Crimea ya haramta'

Zauren babban taron Majalisar Dinkin Duniya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashe 100 ne suka amince da kudurin

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kuduri da ya bayyana kuri'ar raba-gardama da Rasha ta goyi bayan aka yi a Lardin Crimea a zaman haramtacciyya.

Hakazalika kudurin, wanda Ukraine ta tsara daftarinsa, ya nuna goyon bayan ga kasancewar Ukraine a matsayin kasa daya.

Kasashen 100 ne dake cikin zauren majalisar suka amince da kudurin; yayin da kasashe 8 suka nuna rashin amincewa, sannan 58 suka ki nuna matsayinsu, ciki kuwa har da China.

Kudurin dai bai da karfi iko irin na doka, sai dai kasashen yamma da ke goyon bayansa na fatan zai kara sa a maida Rasha saniyar ware ta fuskar diplomasiyya.

Karin bayani