An kusan kawar da Polio a duniya - WHO

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Nigeria da Pakistan da Afghanistan ne ake fama da cutar Polio

Hukumar Lafiya ta Duniya-WHO ta ce yanzu babu cutar shan-inna wato Polio a kashi tamanin cikin 100 na kasashen duniya.

Hakan na zuwa ne bayan kwashe shakaru uku ba a samu ko mutum daya da ya kamu da cutar ba a kasar Indiya.

Hukumar ta WHO ta ce yanzu an samu kakkabe cutar da ilahirin yankin kudu masu gabashin Asiya wanda ya kunshi kasar ta Indiya.

Tun tsakiyyar shekarun 1990 indiya ke gudanarda gagarumin aikin rigakafin cutar inda aka yi wa yara miliyan 170.

Ana dai ganin wannan sanarwa a matsayin babban ci gaba a yakin da ake yi da kwayar cutar mai hadari.

Sai dai har yanzu akwai kwayar cutar wadda ke gurgunta dan adam a kasashen Najeriya da Pakistan da Kuma Afghanistan.

Karin bayani