An sauya salon binciken jirgin Malaysia

Iyalan pasinjojin da ke cikin jirgin Malaysia da ya bata Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Har yanzu 'yan uwan pasinjojin ba su fidda tsammani kan gano wani abu da zai sada su da iyalansu ba.

Jami'an kasar Australia da ke jagorantar binciken jirgin Malaysia da ya bata sun sanar da matsawa daga kudancin tekun India dan ci gaba da bincike.

Sabon Wurin da aka maida hankali a kai yana da misan kilomita dubu daya da dari daya daga ainahin inda ake bincike a wajen.

Hukumar kula da tsaron jiragen ruwan Australia ta ce ta dauki wannan mataki ne sakamakon wasu bayanai da aka samu daga Malaysia.

A ci gaba da nazarin da kasar take yi kan bayanan na'urar da ke sa ido kan zirga-zirgar jiragen sama kafin ya bata.

A yanzu dai hasashen cewa jirgin ya na matukar gudu ne, kuma ta yiwu mansa ya kare ne da wuri.