Gwamnatin Italiya za ta yi gwajon motoci

Hakkin mallakar hoto ebay
Image caption Wasu daga motocin da za ayi gwajon su

Gwamnatin Italiya ta soma gwanjon wasu motocinta da manyan ma'aikatan gwamnati suke amfani da su.

Za a yi gwanjon motocin ne a dandalin cinikayya na EBay wanda ake samu a shafin intanet.

Wannan dai wani mataki ne da Praminista, Matteo Renzi ya dauka na rage kashe kudaden gwamnati.

Daga ranar 16 ga watan Aprilu ne dai za'a soma sayar da motocin.

Kuma tun daga lokacin da aka bayyana shirin sayar da motocin ake ci gaba da samun tayin sayen motocin sosai.

Motocin dai guda dubu daya ne da dari biyar da amfaninsu ba shi da matukar muhimmanci ga gwamnati.

Tuni dai aka bayyana jerin motoci 151 da suka hada da kirar BMW, Alfa Romeo da kuma Lancia, kuma akwai manyan motoci na kasaita kamar kirar Jaguar.

Shirin sayar da motocin dai wani yunkuri ne na Praminista, Matteo Renzi da ya ce, motocin gwamnati sun zama wata alamar almubazzaranci da kudin gwamnati.