'Yara na fama da karancin abinci a Nigeria'

Shugabar Save the children, Jasmine Witbred
Image caption Shugabar Save the children, Jasmine Witbred

Kungiyar bayar da agaji ga kananan yara ta Save The children ta ce, kimanin kashi 37 cikin dari na yaran Najeriya na fama da matsalar rashin isasshen abinci.

Hakan a cewar kungiyar na haddasa wa yaran rashin girma da kuma rashin kaifin basira, abin da zai cigaba da shafarsu har zuwa karshen rayuwarsu.

Shugabar Save the Children Jasmine Whitbred ta shaida wa taron manema Labarai a Abuja cewa "Manyan abubuwan da suka jawo hakan shi ne rashin rungumar tsarin shayar da nonon uwa zalla daga haihuwa zuwa wata shida, domin kasa da kashi 20 cikin dari na iyaye ne ke aiki da tsarin a kasar."

Kungiyar na kuma bai wa yaran da suka kamu da tamowa magani, inda take aiki a jihohi 16 na Najeriya a kowane mako, ko a bara kawai kungiyar ta tallafa wa yara miliyan biyar da iyayensu.