An kashe 'yan Taliban a Kabul

Hakkin mallakar hoto AFP Getty

A Afghanistan an kashe mayakan Taliban wadanda su ka kai wa hedikwatar hukumar zaben kasar hari a birnin Kabul.

Jami'an gwamnati sun ce sun kwato hukumar zaben kasar bayan da su ka kashe dukkan mayakan da su ka kai harin.

Lamarin dai ya zo ne mako guda kafin zaben shugaban kasar.

Hukumomi sun ce 'yan bindiga biyar ne su ka yi shigar mata, su ka boye bindigogi da gurnet-gurnet cikin tufafinsu, su ka kai harin.

Amma bayan an kwashe awoyi hudu ana musayar wuta ne jami'an tsaron su ka kashe su.

Wutar da ta tashi a wurin kuma ta kone wasu akwatunan zabe.

Jim kadan bayan da aka kai harin, shugaban hukumar jin koke-koke gameda zaben, Abdul Satar Saadat, ya bayyana damuwa akan batun.

Yace: "Wannan babban abun damuwa ne. Kamar yadda kasani, Taliban sun yi gargadin cewa za su kai wa kowace runfar zabe hari. Sun gargadi dukkan ma'akatan zabe, kuma sun fara kai wa ma'aikatanmu da ofisoshimu hari.

"Ina fatan gwamnatin Afghaninstan za ta warware matsalar tsaron bada dadewa ba".

Shi kuwa ministan kula da harkokin cikin gida, Omar Daudzai, cewa ya yi matsalar tsaro ba za ta shafi zaben ba.

Yace: "Ban damu ba. Ina tsaye daram, Ina da tabbacin cewa za a tsaurara matakan tsaro daga yanzu har zuwa ranar zabe. "Muna tsakiyar yaki ne.

"A cikin shekaru 12 da su ka wuce, yaki nan bai kare ba. Amma wadannan hare haren ba za su tauye shirin zaben ba," inji shi.

'Yan Taliban dai sun ce sune su ka kai harin. Wannan ne kuma hari na hudu da aka kai a Kabul cikin kwanaki takwas.

Karin bayani