Borno: An kashe mutane 4 a Azir

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rahotanni na cewa an kone kusan rabin kauyen Azir

'Yan bindigar wadanda suka je garin akan babura sun bude wuta da tsakar daren ranar Asabar a lokacin da mazauna kauyen suke bacci inda suka kashe mutane akalla hudu tare da jikkata wasu mutane bakwai.

Wani dan jarida da bai so a ambaci sunansa ba ya shaidawa BBC cewa 'yan bindigar sun kone kusan rabin kauyen kuma akasarin mazauna kauyen sun tsere.

Harin a cewar rahotannin na zuwa ne bayan wata wasika ta gargadi da aka aikewa mazauna kauyen dake cewa za a kai masu harin.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin rundunar sojojin dake aikin tabbatar da zaman lafiya a jahar Borno, sai dai kakakin rundunar sojojin bai amsa wayar sa ba.