china na sabon binciken jirgen Malaysia

Matukin jirgin Malaysia da ya bata Kaftin Zaharie Ahmad Shah Hakkin mallakar hoto Divulga
Image caption Makwanni uku kenan da kasashen duniya suka hada karfi da karfe wajen neman jirgin,amma har yanzu babu amo babu labarinsa.

Jirgin ruwan China ya na bincike a kudancin Tekun India, da fatan a samu wasu daga cikin tarkacen jirgin Malaysia da ya bata makwanni uku da suka gabata.

Shi ne jirgi na farko da ya isa sabon wurin da ake bincike da hukumomin Australia suka gabatar a jiya juma'a, bayan binciken da ya gano cewa man jirgin samfurin Boen 777 ya kare da wuri.

Jirgin Chinan ya na kokarin isa inda aka gano wasu abubuwa masu kama da tarkacen jirgin a jiya juma'a.

Har wayau jirage an samu karin jiragen sama na kasashe biyar da za su shiga cikin binciken jirgin a yau.

Jirgin mallakar kasar Malaysia dai na dauke da pasinjoji da ma'aikata kusan dari biyu da arba'in a lokacin da aka neme shi aka rasa.