Sarakuna: A daina watsi da shawarar mu

Sarakunan Nijeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarakunan Nijeriya

A yayin da ake fama da matsalolin tsaro a wasu sassa na Najeriya,wasu sarakuna a kasar na ganin ya kamata a daina sakaci akan shawarwarin da sukan bayar ko kuma abubuwan da sukan yi wa gwamnati ko jami'an tsaro hannun- ka- mai- sanda, a kokarin da ake yi na kare jama'a da hare hare da sauran matsaloli na tsaro.

Sarakunan wadanda suka hadu a kaduna kwanan nan domin tattauna matsalar tsaron da ake fama da ita a jihar ta Kaduna sun ce a matsayin su na iyayen kasa sukan ga abubuwa da dama masu kama da barazanar tsaro.

Karin bayani