An tsananta binciken jirgin Malaysia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Daya daga cikin jiragen ruwan China da ke laluben jirgin saman Malaysia da ya bace.

Kasashen duniya na tsananta bincike don gano jirgin Malaysian nan da ya bace, inda yanzu haka jiragen sama 10 da na ruwa takwas ke aikin binciken a kudancin Tekun India.

Wani jirgin ruwan Australia da ke iya gano na'urar nan ta black box da ke nadar bayanai cikin jirgin sama, ko da kuwa ta kai zurfin kilomita shida a cikin teku, ya shiga sahun masu binciken.

A ranar Asabar, an kwaso wasu tarkace daga cikin ruwan, amma babu wanda aka tabbatar daga cikin jirgin da ya bata su ke.

Wasu daga cikin dangin fasinjojin 'yan kasar China sun je Kuala Lumpur, babban birnin Malaysia, inda jirgin ya tashi makonni uku da suka wuce.

Karin bayani