An kashe mutane 21 a shalkwatar SSS

Hakkin mallakar hoto AP

Hukumar tsaron farin kaya ta SSS a Najeriya ta ce mutane 21 ne aka kashe a wani yunkurin da wasu da take tsare dasu su ka yi na tserewa daga hedikwatarta a Abuja.

Har yanzu dai babu wani haske akan ko dukkan wadanda aka kashe din mutane ne da hukumar ke tsare dasu.

Mai magana da yawun hukumar, Marilyn Ogar, ta kuma ce jami'an hukumar biyu sun samu munannan raunuka a lamarin

Ga cewarta, wani daga cikin wadanda ake tsare da sun ne ya yi yunkurin kwace makami daga wani jami'in hukumar lokacin da ya shiga ba su abinci.

Ta ce daga nan ne abin ya fara, sai sojoji su kai dauki domin shawo kan matsalar.

An da ta jin karar harbe harbe a hedikwatar hukumar, wadda ke kusa da fadar shugaban kasar.

Kakakin Shugaba Goodluck Jonathan ya ce batun bai shafi fadar shugaban kasa ba.

Jami'an tsaro dai sun tattare hanyoyin shiga fadar shugaban kasar da wadanda ke kusa da hedikwatar hukumar ta SSS.

An kuma dauki tsauraran matakan tsaro a Otel din Transcorp Hilton, inda ministocin kudi na kasashen Afrika ke gudanar da wani taro a kasar.

Wasu kafofin yada labarai a Najeriyar sun ce wadanda su ka yi kokarin tserewa daga hedikwatar hukumar SSS din 'yan Boko Haram ne. Amma hukumomi ba su tabbatar da hakan ba.

Karin bayani