Najeriya: An yi harbe harbe a hedikwatar SSS

Hakkin mallakar hoto AFP

Hukumomin Najeriya sun ce wasu da ake tsare da su a hedikwatar hukumar tsaro ta SSS dake Abuja sun yi yunkurin tserewa.

Mai magana da yawun hukumar SSS, Marilyn Ogar, ta ce lamarin ya faru ne lokacin da wani wanda ake tsare da shi ya daki wani ja jami'in hukumar da ankwar da ke hannunsa.

Ta ce sojoji sun kai dauki domin shawo kan matsalar.

An dai ta jin karar harbe-harbe a wurin, wanda ke kusa da fadar shugaban kasar.

Kakakin Shugaba Goodluck Jonathan ya ce batun bai shafi fadar shugaban kasa ba.

Jami'an tsaro dai sun tattare hanyoyin shiga fadar shugaban kasar da wadanda ke kusa da hedikwatar hukumar ta SSS.

Wasu kafofin yada labarai a Najeriyar sun ce wadanda su ka yi kokarin tserewar 'yan Boko Haram ne.

Karin bayani