Ebola: Senegal ta rufe iyakarta da Guinea

Hakkin mallakar hoto

Kasar Senegal ta rufe iyakar ta da Guinea a wani yunkurin hana yaduwar Ebola, cutar da ta kashe akalla mutane 70.

Hukumomin Senegal din sun ce iyakar zata kasance a rufe har abunda hali yayi...duk da cewa yan kasuwa ke yawan amfani da ita

Yawancin wadanda suka kamu da cutar naa kudancin Guinea ne, amma kuma an tabbatarda cewa wasu mutane sun kamu da cutar a Konakry babban birinin kasar.