An sako 'yan jaridar da aka kama a Syria

Hakkin mallakar hoto N
Image caption An sako 'yan jaridar ne bayan watanni shida a tsare.

An sako wasu 'yan jarida 'yan kasar Spain guda biyu da wata kungiyar mayaka mai alaka da al-Qaeda ta kama a Syria watanni shida da suka wuce.

Jaridar El Mundo ta Spain, ta ce daya daga cikin 'yan jaridar, wanda shi ne wakilinta a gabas ta tsakiya, Javier Espinosa - ya sanar da kamfanin jaridar ta wayar tarho cewa an sako shi tare da mai daukar hoto, Ricardo Garcia Vilanova.

Mr Espinosa ya ce an mika su ne ga sojojin Turkiyya.