'Illar sauyin yanayi za ta tsananta'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption karancin abinci shi ne babban abin damuwa, inda dumamar yanayi ta fara tasiri kan amfanin gona.

Wani sabon bincike da aka yi kan sauyin yanayi ya yi gargadin cewa, bil'adama na kara jin illar da zai kasance mai tsanani da ba za a iya jure wa ba.

Rahoton ya ce daruruwan miliyoyin bil'adama za su fuskanci bala'in ambaliyan ruwa, kuma lamarin ka iya haddasa bazuwar cututtuka cikin sauri.

Wani kwamitin gwamnatocin kasashen duniya, mai nazarin sauyin yanayi ne ya fitar da wannan sakamakon, ranar Litinin a kasar Japan.

Kwamitin dai ya yi nazari kan sakamakon bincike-bincike mafiya inganci, daga masana dari uku da tara wadanda suka fito daga kasashe 70 na duniya.

Karin bayani