Kotu ta kori 'yan majalisa da suka koma APC

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jam'iyyar PDP da ta APC na hammaya na juna

Wata babbar kotun tarayya a Abuja dake Nigeria ta yanke hukuncin cewar 'yan majalisar wakilai 37 da suka bar PDP suka koma jam'iyyar adawa ta APC, su sauka daga kujerunsu na majalisar wakilan.

Alkalin kotun, Mai shari'a Adeniyi Ademola ya ce 'yan majalisar su ajiye mukamansu saboda sauya sheka daga jam'iyyar da aka zabesu cikin ta.

A cewar kotun daga yanzu, 'yan majalisar ba suda hurumin tafka mahawara a kan abubuwan dake gudana a zauren majalisar.

A cikin watan Junairu ne jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta shigar da kara gaban kotu don kalubalantar matakin 'yan majalisar da suka canja zuwa jam'iyyar APC.

Kawo yanzu dai 'yan majalisar da hukuncin kotun ya shafa basu mayar da martani ba.

Karin bayani