An ki bada belin 'yan Al Jazeera a Masar

Image caption An gudanar da zanga-zanga a kasashe daban-daban na duniya dun a saki 'yan jaridar.

Wata kotu a Masar ta ki ta bada belin 'yan jaridan nan uku dake yiwa gidan talabijin na Al Jazeera, aiki, wadanda ake tuhuma da yada labaran karya da kuma taimakawa haramtacciyar kungiyar nan ta 'yan Uwa Musulmi.

A zaman shariar baya-bayan nan dai, an baiwa 'yan jaridar da ake tuhuma, damar fitowa daga kajin da ake tsare da su, domin yin magana kai tsaye da alkali.

'Yan jaridar, wadanda ake tsare da su tun cikin watan Disambar bara, sun hada da tsohon ma'aikacin BBC, Peter Greste, wanda dan kasar Australia ne da kuma Shugaban Ofishin Al Jazeera dake Alkahira, Mohamed Fahmy.

Yanzu dai an dage shari'ar ta su har zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.

Karin bayani