Ana musayar wuta tsakanin Koriya da Koriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babu dai wani martani daga Koriya ta Arewa har yanzu.

Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu sun yi musayar wuta a kan iyakarsu ta ruwa.

Hukumomin Koriya ta kudu sun ce lamarin ya faru ne bayan da dakarun Arewa suka harba rokoki zuwa Kudu a lokacin da suke atisaye.

Mahukuntan kudun sun ce jami'ansu sun mai da martani ne.

Rahotanni kuma sun ce an umarci mazauna wani tsibirin kan iyaka da ke kudancin Koriya da su shiga mafakar bama-bamai don gudun abin da ke iya faruwa.

Karin bayani