An kashe fararen hula talatin a Jamhuriyar tsakiyar Afrika

Sojan sa kai na Kirista, anti Balaka Hakkin mallakar hoto
Image caption Sojan sa kai na Kirista, anti Balaka a Jamhuriyar tsakiyar Afrika

'Yan sanda a jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun ce, an kashe mutane akalla talatin, kuma aka jikkata wasu mutanen goma yayin fada tsakanin wasu kungiyoyin Krista da na Musulmi.

Jami'an gwamnati sun ce, yawancin wadanda suka mutu a garin na Dekoa dake tsakiyar kasar fararen hula ne da tsautsayi ya fada kansu.

Kungiyar Kristoci ta anti-Balaka ce ta kai hari a wurin da 'yan kungiyar Seleka ta musulmi suke da iko.

Tuni dai dakarun kiyaye zaman lafiya na Faransa suka zafafa sintiri a Bangui babban birnin kasar.