'Yan Guinea da Liberia ba za su hajji ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cutar Ebola ta bulla a kasashen Guinea da Saliyo da kuma Liberia

Hukumomin Saudiyya sun ce, ba za su bada vizar zuwa aikin Hajjin bana ba ga maniyyatan kasashen Guinea da kuma Liberia saboda barkewar cutar Ebola a wadannan kasashen.

Cutar Ebola dai tana kashe kashi casa'in na wadanda suka kamu da ita.

Tuni dai dama, hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta bada shawarar hana tafiya zuwa kasashen Liberia, da Guinea da kuma Saliyo inda aka bada rahotannin bullar cutar.

Itama kungiyar agaji ta likitoci Medicin San Frontiers ta fadi cewa, cutar ta Ebola ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 78 a kasar Guinea tun daga watan Janairu.

Kuma wannan shi ne karon da cutar ta fi yin barna, yayin da kuma ake ci gaba da fargabar cewa, cutar za ta iya yaduwa zuwa wasu kasashen yammacin Afurka.

Karin bayani