Hari: An cafke mutane 200 a Kenya

Wata wacce ta ji rauni a harin Nairobi
Image caption Kawo yanzu babu wata kungiya ko wani wanda ya dauki alhakin kai harin, amma ana zargin Al-shabab

'Yan sanda a Kenya sun cafke fiye da mutane 200, bayan wani hari da aka kai a ranar Litinin da maraice, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane shida.

Mutane da dama ne suka jikkata a yayin da wasu abubuwa suka fashe sau uku a lokaci guda a gundumar Eastleigh, inda mafi yawan mazauna gurin 'yan Somalia ne.

'Yan sanda sun ce akwai yiwuwar an yi amfani da gurneti da kuma bam da aka hada a harin, wanda aka kai kan wani gidan abinci da asibiti.

Biranen Nairobi da Mombasa mai tashar jiragen ruwa, sun sha ganin hare-hare irin wannan a 'yan watannin baya-bayan nan, hare-haren da 'yan sanda ke zargin masu fafutukar Islama da kai wa.