Hukumar zabe na sake fasalta mazabu a Nigeria

Shugaban hukumar zaben Najeriya, farfesa Attahiru Jega
Image caption A shekarar 2015 ne za a yi babban zabe a Najeriya

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC za ta fara sake fasalta mazabu, abin da zai iya shafar 'yan majalisar wakilai da na jihohi.

Idan ta kammala aikin hakan zai sa wakilan wasu jihohi su karu a majalisar dokoki na kasa a zabe mai zuwa.

Aikin sake shata mazabun na zuwa ne shekaru 18, bayan na karshe da aka yi a shekarar 1996.

A halin yanzu dai kasar na da mazabu 388, kuma kudin tsarin mulkin Najeriya ya ce a dinga sake fasalta mazabun duk bayan shekaru 10.