Kamaru ta kama ministan ilimin sakandare

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Kamaru, Paul Biya.

A Jamhuriyar Kamaru, jami'an tsaron sun cafke Ministan kula da ilimin sakandare Louis Bapes Bapes kafin a gurfanar da shi a gaban kuliya a wani yunkuri na neman tabbatar da mulki na gari.

Kawo yanzu dai babu tabbaci game da abinda ake tuhumar shi da aikatawa, amma kuma ana kiyautata zaton cewa Ministan ya yi almubazzaranci da kudaden kasa, da kuma yin sama da fadi da tarin wasu, ganin cewa ya fara gurfana a gaban kotu ta musamman mai shari'a akan aikata manyan laifuffuka wadda aka kafa a bara.

Ministan dai shi ne mutum na biye mai rike da mukamin mulki da aka gurfanar gaban kotun musamman mai yaki da cin hanci da rashawa.

Karin bayani