Miliyan bakwai sun yi rajistar Obamacare

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shirin dai na da bakin jini sosai tsakanin masu zabe a kasar.

Dubban daruruwan Amurkawa ne suka sa hannun don shiga shirin inshorar lafiya na Shugaba Obama ranar Litinin; a kokarin samun shiga cikin shirin kafin wa'adin aka deba don rufe yin rijistar ya cika .

Jami'an gwamnatin kasar sun ce sun cimma adadin mutanen da suke neman su sa hannu domin shiga shirin wato mutane miliyan bakwai.

Abokan kawancen Obama sun ce shirin na Affordable Care Act zai kawo ayyukan kiwon lafiya kusa ga wadanda suka fi bukatar su; amma 'yan jam'iyyar Republican sun ce tsabage barnar kudi ne.

Wannan shirin dai na daya daga cikin manufofin kyautata jin dadin jama'a na gwamnatin Obama da suka raba kawunan 'yan siyasar kasar, kuma zai zama babban batu a zabubukan tsakiyar wa'addi da za a yi a watan Nuwamba.

Karin bayani