An zargi Sanusi da tallafawa Boko Haram

Image caption Sanusi Lamido Sanusi ya musanta zargin da ake ma sa.

Gwamnatin Najeriya ta zargi gwamnan babban bankin kasar, Malam Sanusi Lamido Sanusi wanda aka dakatar da samar da kudi ga aikace-aikacen kungiyar nan da wasu ke kira Boko Haram.

Lauyin gwamnatin Fabian Ajagu ne ya bayyana hakan a zaman da wata babbar kotu ta tarayya dake Lagos ke ci gaba da bin bahasin karar da Malam Sanusi Lamido Sunusi ya shigar game da kwace masa fasfo.

Sai dai lauyan gwamnan babban bankin Barrister Kola Awodein ya musanta zargin gwamnatin cewa yana taimakawa kungiyar Boko Haram inda ya kalubalanci gwamnatin da ta kawo shaida.

Za a ci gaba bin bahasin shari'ar ranar Alhamis a Lagos.

Karin bayani