CAR za ta kankane taron Afrika da Turai

Tashin hankali ya munana a Afrika ta Tsakiya
Image caption Za a kwashe Musulmi dubu 19 daga Afrika ta Tsakiya

Tashin hankalin da ake fama da shi a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, zai yi kane-kane a taron Afrika da nahiyar Turai da za a bude a Brussels a ranar Laraba.

Taron ya zo ne bayan kungiyar tarayyar Turai ta kaddamar da dakarunta su 1,000 da aka samu jinkirin tura wa Afrika ta Tsakiya.

Kasancewar rundunar tarayyar Afrika 6000 da na Faransa 2,000 bai hana cigaba da tashin hankali a kasar ba.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon da shugabannin kasashe 30 daga nahiyoyin biyu, za su yi gana wa game da tashin hankalin Afrika ta Tsakiya, kafin a fara taron kolin.

Shugabar hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Navy Pillay ta yi gargadin cewa kiyayya tsakanin musulmi da Kirista ta kai halin ha ula'i a Afrika ta tsakiya.