Ghana: Gwamnati ta tsuke bakin aljihu

Image caption John Mahama, shugaban Ghana

Gwamnatin Ghana tace ta soma daukar tsauraran matakan tsuke bakin aljihu don shawo kan tabarbarewar da tattalin arzikin kasar yake ci gaba da yi.

A jawabin da yayi kan halin da tattalin arzikin kasar yake ciki a zauren majalisar dokokin kasar jiya ministan kudi, Seth Tekper ya fayyace matakan tsuke bakin aljihun.

Yace, matakan sun hada da dakatar da cin bashi daga kasashen waje da kuma dakatar da daukar sabbin ma'aikata aiki.

Ministan ya kuma ce, gwamnati ta dakatar da karin albashi ga ma'aikatanta.

Cikin 'yan watannin nan tattalin arzikin Ghana ya shiga tsaka mai wuya.

Darajar kudin kasar Cedi ta fadi sosai, yayin da kuma farashin kaya ya tashi.