Harin Bam a Masar ya kashe babban 'dan sanda

Wurin da aka kai harin bam a Masar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bama-bamai biyu sun tashi kusan lokaci daya, amma na ukun sai bayan sa'oi biyu ya tashi

Wani babban dan sanda ya rasa ransa, a wani harin bam da aka kai kusa da jami'ar Alkhahira da ke Masar a ranar Alhamis.

Yayin da wasu mutane biyar kuma suka jikkata a lokacin da bama-bamai uku suka tashi a birnin.

Wata kungiya dake kiran kanta Ajnad Misr, ko sojojin Masar ce ta dauki alhakin kai harin.

An samu karuwar kai hare-haren masu tayar da kayar baya a Masar, tun bayan hambarar da gwamnatin Muhammad Morsi a shekarar 2013.