Za a ba wadanda hari ya shafa N100 miliyan

Gwamnan Katsina,  Shehu Shema Hakkin mallakar hoto AFP

Gwamnatin jihar Katsina a arewacin Nigeria tace, zata bawa wadanda rikicin da aka yi a jihar ya shafa gudunmuwar naira miliyan 100.

Hakan a cewar gwamnatin mataki ne na saukaka musu radadin halin da suka shiga sanadiyyar harin na watan jiya.

Wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan jihar na Musamman ya fitar tace, cikin wadanda za a bawa taimakon har da 'yan sanda uku da suka rasa rayukansu yayin tarzomar, da kuma baturen 'yan sandan yankin Faskari da aka jikkata.

Sama da mutane 100 ne dai suka rasa rayukansu, wasu kuma suka jikkata a wasu hare-hare da wasu 'yan bindiga suka kai, kananan hukumomin Faskari da Sabuwa a jihar ta Katsina.