Mutane 8 sun mutu a kwale-kwale a Lagos

Hakkin mallakar hoto Google Maps
Image caption An bana a samu rasuwar mutane da dama sakamakon kifewar jirgin ruwa a Nigeria

Wani kwale-kwale ya kife a Jihar Lagos dake kudancin Nigeria, lamarin da ya janyo mutuwar mutane takwas.

Kwale-kwalen ya kife ne bayan da ya ci karo da dutse a cikin ruwa a ranar Laraba, amma kuma an samu damar ceto sauran mutane 12 dake cikinsa.

Hukumar agajin gaggawa ta kasar NEMA wacce ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta ce kwale-kwalen ya taso ne daga Ebute-Ero yana kan hanyarsa ta zuwa Ikorodu dake yankin arewacin jihar ta Lagos.

Wannan hadarin ya afku ne makwanni uku bayan da wani jirgin ruwa na katako ya kife a kusada garin Festac na Lagos din , inda mutane 13 suka mutu.

Daukar mutane fiye da kima a jiragen ruwa ya zama ruwan dare a Nigeria, saboda kokarin masu kwale-kwale na cin riba mai yawa.