Takardun bogi na rashin HIV a Uganda

Allunan wayar da kan mutane kan cutar HIV a Uganda Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A shekarar 2005 Uganda ta samu rage daukar cutar HIV zuwa kashi shida cikin dari

Kasuwar bayan fage na sayar da shaidar likita da ke tabbatar da cewa mutum ba ya dauke da cutar HIV ga masu dauke da cutar na bunkasa a Uganda.

Ana nuna tsangwama sosai ga mutanen da ke dauke da cutar HIV a kasar, kuma suna shan wuya wajen samun aiki.

Wani dan jarida mai zaman kansa Matthew Stein ya yiwa sashen Africa na BBC bincike a kan takardun bogi na likitoci.

Asibitoci 12 cikin 15 da aka ziyarta a Kampala lokacin binciken sun bayar da takardun likita na bogi ga masu cutar HIV, a kan kudi dalar Amurka 20 zuwa 100.

A farkon shekarar 1999 kasar Uganda na sahun gaba a cikin kasashen da al'umarta ke da cutar HIV, inda kashi 20 cikin dari na mutanen kasar ke dauke da kwayar cutar.